An kama wata mahaukaciyar bogi da jikin ‘Dan Adam a Legas

An kama wata mahaukaciyar bogi da jikin ‘Dan Adam a Legas

Labari ya zo mana cewa an yi ram da wata mahaukaciyar karya dauke da gawan mutum da ma wasu bangarori na jikin ‘Dan Adam a karkashin wata gada a Yankin Ojo da ke cikin tsakiyar Garin Legas.

An kama wata mahaukaciyar bogi da jikin ‘Dan Adam a Legas
Sufeta Janar na 'Yan Sandan Najeriya Ibrahim Idris
Asali: Depositphotos

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa asirin wata mahaukaciyar karya mai suna Folake Folade ya tonu a Ranar Litinin dinnan inda aka gano cewa ashe lanbo ta ke yi kamar mai cutar haukan gaske bayan tayi sama da shekaru 9 tana wannan aiki.

Binciken da aka soma ya nuna cewa Folake Folade ba mahaukaciya bace kuma ta kan fito kamar karuwa mai zaman kan ta domin jawo maza. Kusan a haka ne wannan Baiwar Allah ta ke yin ram da mazaje tana cire sashen jikin su.

KU KARANTA: 'Yan luwadi za su ji dadi a Gwamnati na - Duke

Labari ya bayyana cewa wannan Baiwar Allah ta kan saidawa jama’a bangarorin jikin mutun a cikin dare a kasan gadar da ta ke zama. Manyan mutane na zuwa ta sa masu sassan jikin mutum a cikin mota ba tare da jama’a sun ankara ba

Wasu na zuwa ne da niyyar kwanciya da wannan mata, da zarar ta taba mutum dai sai ya rasa hayyacin sa. A haka ne ta ke yin abin da ta ga dama da su har ta saidawa manyan mutane bangarorin jikin su kafin Allah ya sa dubun ta su cika.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel