Kwallon Ronaldo ta fi kowace kyau a shekarar 2018 – UEFA

Kwallon Ronaldo ta fi kowace kyau a shekarar 2018 – UEFA

Kwallon da ‘Dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo ya ci a shekarar nan ce ta lashe kyautar kwallon da ta fi kyau a kaf kakar da ta wuce kamar yadda Hukumar kwallon kafa ta Turai ta bayyana.

Kwallon Ronaldo ta fi kowace kyau a shekarar 2018 – UEFA
An zabi kwallon Ronaldo a matsayin wanda ta fi kyau a bana
Asali: Getty Images

A bana ne Cristiano Ronaldo ya ci Juventus wata kwallo da ta ba jama’a mamaki inda yayi tsalle ya watse ta baya har cikin ragar Gianluigi Buffon. Wannan kwallo aka zaba a matsayin wanda ta fi kowace kwallo kyau a 2018.

Sama da mutane 200, 000 cikin mutane 346, 915 da su ka shiga shafin UEFA su ka zabi kwallon da tsohon ‘Dan wasan Real Madrid Ronaldo a Turai. A bara ma dai ‘Dan wasan Juventus Mario Mandžukić ne ya lashe kyautar.

KU KARANTA: Dan wasa Ronaldo ya sa gidan sa da ke Sifen a kasuwa

Ronaldo ya ci Juventus a Gasar Zakarun Nahiyar ne lokacin yana bugawa Real Madrid. Kwallon ‘Dan wasan Marseille Dimitri Payet ce ta zo na biyu yayin da kwallon da Eva Navarro ta ci a wasan Sifen da Kasar Jamus ta zo 3.

Kwanan nan kun ji cewa Gwarzon ‘Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa tafin da Magoya bayan Juventus su ka yi masa a lokacin da ya zura kwallo a ragar su ce ta sa ya koma taka leda a Kungiyar a shekarar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel