Takarar shugaban kasa: Kwankwaso yayi zargin gwamnatin tarayya na masa bita da kulli

Biyo bayan hana shi filin taron daya nema domin kaddamar da takararsa ta shugaban kasa, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yace duk bita da kullin da za’ayi a yi, amma fa babu gudu babu ja da baya.

Jaridar daily trust ce ta ruwaito kaakakin Sanata Kwankwaso, Hajiya Binta Sipikin tana cewa babu wani barazana ko bita da kullin da zai yi tasiri akan Kwankwaso har ta kai ga ya fasa kaddamar da takararsa.

KU KARANTA: Takarar shugaban kasa: Kwankwaso ya sanar da sabon dandalin da zai kaddamar da takararsa a Abuja

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamitin yakin neman zaben Sanatan tana cewa a ranar Talata ta samu wasika daga manajan kamfanin dake kula da dandalin Eagles Square cewa an hanasu gudanar da taron a wurin, don gudun kada su takura ma ma’aikata duk da sun biya kudinsu tun mako guda daya wuce.

Takarar shugaban kasa: Kwankwaso yayi zargin gwamnatin tarayya na masa bita da kulli
Kwankwaso
Asali: Facebook

“Mun ji mamakin wannan mataki da gwamnati ta dauka, kuma mun kalli wannan lamari a matsayin bita da kulli da gwamnati ke yi mana sakamakon ta lura tafiyar Sanata Kwankwaso na samun tagomashi, wanda hakan ba zai haifar ma dimukradiyya da mai ido ba.” Inji kwamitin.

Bugu da kari wani daga cikin abokan siyasar Sanata Kwankwaso, Alhaji Haruna Umar Doguwa yace: “Mun cika wasu ka’ida da sharudda da ake bukata don amfani da wannan dandali, kwatsam sai muka samu labarin an turo oda daga sama cewa kada a barmu muyi taron, amma da su sani wannan zaluncin ba zai hana Kwankwaso kaddamar da takararsa ba

“An hana mu shiga Kano, yanzu kuma an hana mu taro a Abuja, ban san dalilin da yasa ake haka a karkashin gwamnatin da tayi alkawarin yin biyayya ga tsarin Dimukradiyya ba.” Inji shi.

A wani labarin kuma wani daga cikin kwamitin yakin neman zaben Kwankwaso, Mohammad Jamo ya bayyana cewa an samu wani sabon wuri da Kwankwaso zai kaddamar da takararsa, inda yace zasu yi amfani da dakin taro na Otal din Chida dake jabi Abuja.

Biyo bayan hana shi filin taron daya nema domin kaddamar da takararsa ta shugaban kasa, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yace duk bita da kullin da za’ayi a yi, amma fa babu gudu babu ja da baya.

Jaridar daily trust ce ta ruwaito kaakakin Sanata Kwankwaso, Hajiya Binta Sipikin tana cewa babu wani barazana ko bita da kullin da zai yi tasiri akan Kwankwaso har ta kai ga ya fasa kaddamar da takararsa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamitin yakin neman zaben Sanatan tana cewa a ranar Talata ta samu wasika daga manajan kamfanin dake kula da dandalin Eagles Square cewa an hanasu gudanar da taron a wurin, don gudun kada su takura ma ma’aikata duk da sun biya kudinsu tun mako guda daya wuce.

“Mun ji mamakin wannan mataki da gwamnati ta dauka, kuma mun kalli wannan lamari a matsayin bita da kulli da gwamnati ke yi mana sakamakon ta lura tafiyar Sanata Kwankwaso na samun tagomashi, wanda hakan ba zai haifar ma dimukradiyya da mai ido ba.” Inji kwamitin.

Bugu da kari wani daga cikin abokan siyasar Sanata Kwankwaso, Alhaji Haruna Umar Doguwa yace: “An hana mu shiga Kano, yanzu kuma an hana mu taro a Abuja, ban san dalilin da yasa ake haka a karkashin gwamnatin da tayi alkawarin yin biyayya ga tsarin Dimukradiyya ba.” Inji shi.

A wani labarin kuma wani daga cikin kwamitin yakin neman zaben Kwankwaso, Mohammad Jamo ya bayyana cewa an samu wani sabon wuri da Kwankwaso zai kaddamar da takararsa, inda yace zasu yi amfani da dakin taro na Otal din Chida dake jabi Abuja.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel