Ku ajiye mukamanku – Gwamna El-Rufai ga jami’an gwamnati dake muradin takara

Ku ajiye mukamanku – Gwamna El-Rufai ga jami’an gwamnati dake muradin takara

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi kira ga dukkanin masu bukatar tsayawa takara a zaben shekarar 2019 daga cikin masu rike da mukamai a gwamnatin Gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufai, inji rahoton jaridar Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin gwamnatin jihar Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Talata, 28 ga watan Agusta, inda ya bayyana dacewar yin murabus din jami’an na gwamnatinsu.

KU KARANTA: Katin zabe: Gwamnatin jahar Zamfara ta sanar da hutun gamagari a ranar Juma’a

“kiran da Gwamna yayi ga jami’an gwamnatinsa dake bukatar tsayawa takara da su yi murabus zai basu daman bin dokokin jam’iyyar APC.” Inji KaakakI Samuel Aruwan.

Sai dai sanarwar bata bayyana sunayen wadanda suke neman tsayawa takara daga cikin jami’an gwamnatin jihar ba, amma Legit.ng ta tabbatar da tsayawa takarara Sanatan Kaduna ta kudu da mataimakin gwamnan jihar, Barnabas Bala Bantex zai yi.

Haka zalika mashawarcin Gwamna El-Rufai akan al’amuran siyasa, Uba Sani ya bayyana burinsa na tsayawa takarar Sanatan mazabar Kaduna ta tsakiya, inda ake sa ran zai fafata da Sanata mai ci, Shehu Sani.

Bugu da kari, kwamishinan hakokin kudi na jhar Kaduna, Suleiman Audu Kwari zai tsaya takarar Sanatan shiyyar Zariya a karkashin inuwar jam’iyyar APC, inda zai fafata da Sanata mai ci, Suleiman Hunkuyi.

Baya ga wadannan da muka ambato, akwai sauran mukarraban gwamnan dake da muradin tsayawa kujerun yan majalisun dokokin jihar Kaduna, daga cikinsu akwai mashawarcin gwamnan akan al’amuran matasa, Auwal Yaro mai Kyau.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel