PDP ta ce Buhari ya gaza, sun zayyana wasu manyan zunuban sa

PDP ta ce Buhari ya gaza, sun zayyana wasu manyan zunuban sa

A wani jawabi da sakataren yada labaran PDP, Kola Ologbondian, ya fitar, ya bayyana cewar hatta yaki da cin hanci da gwamnatin Buhari ke tutiya da shi na bogi ne da ake amfani da shi domin muzgunawa 'yan jam'iyyar adawa.

A jiya, Lahadi, ne jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewar hatta shugaba Buhari da kan sa ya san ya gaza.

PDP ta bayyana cewar shugaba Buhari ya gaza ta kowanne bangare kamar yadda rahotanni a gida da ketare suka nuna.

"Wannan gwamnati dake ikikrarin yaki da cin hanci ba wani abu suke yi ba sai karya da yaudarar jama'a domin gwamnati ce dake cike da masu cin hanci, karyar takardun karatu, masu aringizon kudin kwangila."

PDP ta ce Buhari ya gaza, sun zayyana wasu manyan zunuban sa
Kola Ologbondian

"Muna son idan har shugaba Buhari mai gaskiya ne ya daina kare hadimansa tare da gudanar da bincike a kan su domin tabbatar da gaskiyar su," a cewar jawabin PDP.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa fadar shugaban kasa ba zata yi raddi ga kalaman Trump a kan Buhari ba

PDP ta ce daga cikin manyan zunuban Buhari akwai raba kan 'yan Najeriya, gaza dakatar da asarar rayuka a sassan Najeriya, taka hakkin 'yan kasa da rashin mutunta tsarin siyasa, cin mutuncin majalisa da jefa kasa cikin halin galabaita.

PDP ta zargi gwamnatin shugaba Buhari da yi mata fashin aiyukan da tayi kokacin da take gwamnati tare da kalubalantar yin fito na fito a kan wacce gwamnati ta fi yiwa Najeriya aiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel