Jiragen yakin rundunar Sojan sama sun tafka ma yan bindiga mummunan asara a Zamfara

Jiragen yakin rundunar Sojan sama sun tafka ma yan bindiga mummunan asara a Zamfara

Rundunar Sojan sama ta sanar da halaka akalla yan bindiga guda Talatin a wani hari da ta kai kauyuka daban daban a jihar Zamfara, kamar yadda kaakakin rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola ya bayyana.

Legit.ng ta ruwaito Daramola ya sanar da haka ne a ranar Lahadi, 26 ga watan Agusta, inda yace Sojojin rundunar sun mayar da hankulansu ne wajen lalata duk wani sansanin yan bindigan, a haka ne suka kashe mutum 30 bayan wasu hare hare da suka kaddamar.

KU KARANTA: Leah Sharibu ta yi magana karo na farko a hannun Boko Haram

“Sojojin rundunar Sojan sama dake aikin ‘Diran mikiya’ sun samu nasarar lalata sansanonin yan bindiga daban daban a kauyukan Dajin Bawa da Sunke, duk a karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara, an shirya hare haren ne bayan samun bayanan sirri dake nuna yan bindigan sun yi gudun hijira daga sassa daban daban zuwa karamar hukumar Anka.” Inji shi.

Daramola ya cigaba da fadin hakan ne ya sanya rundunar amfani da na’urorin tattara bayanai na zamani wajen tabbatar da sabon mabuyar yan bindigan, a haka suka gano sansanonin a kauyukan Dajin Bawa da Sunke, inda suka yi musu ruwan wuta da yayi sanadiyyar mutuwar mutum 30, da dama suka jikkata.

Daga karshe Kaakaki Daramola yace rundunar sojin sama za ta cigaba da mamaye yankin don tabbatar da tsaro tare da dawowar zaman lafiya mai daurewa a yankin.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba ma rundunar Sojan sama bisa kokarin da take yi wajen kawo karshen ayyukan yan bindiga a jihar Zamfara ta hanyar yakarsu da jiragen yaki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel