Duba da kan ka: Hukumar zabe ta saki sakamakon zaben kananan hukumomin jihar Imo

Duba da kan ka: Hukumar zabe ta saki sakamakon zaben kananan hukumomin jihar Imo

A yau ne hukumar zabe a Imo ta saki ilahirin sakamakon zaben kananan hukumomin jihar da aka kammala a jiya, Asabar.

Jam'iyyar APC mai mulki a jihar ta Imo ce ta lashe zaben a fadin kananan hukumomi 27 da jihar ta Imo ke da su.

Ethelbert Ibebuchi, shugaban hukumar zabe ta Imo, ne ya sanar da hakan a yau, Lahadi, a Owerri, babban birnin jihar.

Duba da kan ka: Hukumar zabe ta saki sakamakon zaben kananan hukumomin jihar Imo
Duba da kan ka: Hukumar zabe ta saki sakamakon zaben kananan hukumomin jihar Imo

DUBA WANNAN: 2019: Dan takarar PDP ya yi tsokaci kan farin jini Buhari a arewa

A cewar wasu rahotanni, jam'iyyun adawa na PDP da APGA sun kauracewa zaben.

Ba wani bakon abu bane jam'iyyar dake da gwamnati a jiha ta lashe dukkan kujerun takara a zaben kananan hukumomi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel