Zan kashe 'yan Boko Haram 1,000 idan na girma na zama soja - wani yaro mai shekaru 12

Zan kashe 'yan Boko Haram 1,000 idan na girma na zama soja - wani yaro mai shekaru 12

- Wani yaro dan shekaru 12 da ke sansanin 'yan gudun hijira, Subairu ya ce yana son ya zama soja idan ya girma

- Sabairu ya dauki alkawarin zai kashe a kalla mayankan Boko Haram 1,000 idan ya zama soja

- Ya kuma yi kira da gwamnatin tarayya ta kawo musu taimako saboda irin matsanancin halin da muke ciki

Wani yaro mai shekaru 12 daga sansanin 'yan gudun hijira da ke Gwoza mai suna Subairu ya ce yana son ya zama soja idan ya girma kuma zai sadaukar da rayurwarsa ne wajen farautar mayakan Boko Haram.

Subairu ya yi alkawarin cewa zai kashe a kalla 'yan Boko Haram 1,000. Ya kuma koka kan irin mawuyacin halin da suke ciki a sansanin 'yan gudun hijirar. Kazalika, Subairu ya bayyan cewa yana kewan 'yan uwansa musamman kakansa da mahaifinsa kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Zan kashe 'yan Boko Haram 1,000 idan na girma na zama soja - wani yaro mai shekaru 12
Zan kashe 'yan Boko Haram 1,000 idan na girma na zama soja - wani yaro mai shekaru 12

Ya kuma yi kira da gwamnatin tarayya ta taimaka ma mazauna sansanin gudun hijirar.

DUBA WANNAN: An dakatar da DPO na 'yan sanda da ya kai samame a masallaci

"Gaskiya ne wasu daga cikinmu bamu da takalma. Idan na girma, ina son in zama soja saboda in samu damar kashe 'yan Boko Haram. Ina son in kashe a kalla guda 1,000. Bamu da komi a nan. Ina kewan Gwoza. Ina kewan mahaifina da kaka na da sauran 'yan uwan na a Gwoza. Bani da kayan makaranta hakan kuma na kawo cikas wajen zuwa makaranta," inji shi.

Wani yaro mai shekaru 12 mai suna Aliyu Bakura ya roki gwamnati a taimaka musu da abinci, kayan makaranta da takalma.

"Malaman mu suna koyar da mu sosai. Suna koyar da mu darrusa da yawa. Ina son in zama likita idan na girma. Ina rokon gwamnati ta taimake mu. Su taimaka mana da abinci, kayan makaranta da takalma," inji Bakura.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel