Riba da amfanin da ke cikin soyaya ko auren mace soja

Riba da amfanin da ke cikin soyaya ko auren mace soja

Samari da dama suna fargaban fara soyaya ko auren mace soja saboda irin labarun da aka dade ana yada wa game da su wanda ake alakantawa da horaswa na aikin soja da suka samu. Galibin mutane na ganin sai sojoji maza kawai ke iya aurensu.

Sai dai wannan lamarin ba haka ya ke ba. Sojoji mata mutane ne kamar sauran mata kuma suna bukatar soyaya da kulawa kamar yada ko wane 'dan adam ko bukata.

Abin dubawa a nan kawai shine irin yanayin fuskar da mutum ya tunkari soyayar da ita, idan mutum ya mutunta kansa to babu shakka suma matata sojojin zasu bashi girma da mutuncin da ya dace.

Riba da amfanin da ke cikin soyaya ko auren mace soja
Riba da amfanin da ke cikin soyaya ko auren mace soja

Ga dai wasu muhimman abubuwa da mafi yawan mutane basu fahimta ba game da soyaya ko auren mace soja:

1. Tausayi da jin kai

So da yawa mutane na tsoron kusantar mace soja saboda tsoran bacin ranta idan an samu rashin jituwa. Sai dai abin mamaki da mutane basu sani ba shine mafi yawancinsu suna da saukin kai da kyayawar alaka da abokansu. Kazalika, su kan iya bawa abokansu da masoyansu kariya idan wata matsala ta taso

DUBA WANNAN: 2019: Rikicin tikitin takarar shugabancin kasa ya raba kan masu ruwa da tsaki a PDP

2. Kiyaye mutuncinsu wajen alaka da abokan aiki

Mutane da yawa suna tunanin mata sojoji sun kan bada kansu ga shugabaninsu domin samun wata alfarma ko karin girma a wajen aiki sai dai wannan lamarin ba haka ya ke ba. Akwai mata sojoji da yawa da ke kame kansu duk da cewa suna aiki tare da maza a lokuta da dama.

2. Kulawa da yara

Kamar yadda sauran mata ke sha'awar haihuwa kuma suke bawa yaransu kulawa sosai, akwai mata sojoji da yawa masu aure da yara kuma sukan mayar da hankali sosai wajen kulawa da yaransu tare da basu tarbiya. Galibi ma basu cika shagawaba yara ba wanda hakan ke sanya yaransu su kasance masu tarbiya sosai.

3. Jure gwagwarmaya da wahalhalun rayuwa

Saboda irin horo ga gwagwarmaya da aikin soja da gada. Mata sojoji suna da matakur juriya wajen fuskantar gwagwarmayar rayuwa kuma sukan bawa mosayansu ko mazajensu goyon baya da kwarin gwiwa da suke bukuta musamman a lokutan da wasu abubuwan masu wahala suka bulo a rayuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel