An dakatar da DPO na 'yan sanda da ya kai samame a masallaci

An dakatar da DPO na 'yan sanda da ya kai samame a masallaci

- Hukumar 'yan sanda ta dakatar da wani DPO da ake tuhuma da kaiwa mutane samame tare da karbar kudadensu

- An dai wallafa labarin DPO ne a jaridu inda aka ce ya tafi masallaci da wasu wurare yana zaluntar mutane yayin bikin sallah

- Wannan tuhumar ya sa Kwamishinan 'yan sandan Legas ya dakatar da DPO don gudanar da bincike a kan lamarin

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Legas, Imohimi Edgal ya bayar da umurnin tsige DPO 'yan sanda mai kula da caji Ofis din Pen Cinema, Harrison Nwabusi sakamakon zargin rashawa da wata jarida ta wallafa ya aikata a ranar bikin Sallah.

An ruwaito cewa DPO mai mukamin Sufritandant na 'yan sanda ya bazama cikin gari na tare da yaransa inda suka rika kai samame ba bisa ka'ida ba suna kwace kudade daga hannun jama'a wanda basu san hawa ko sauka ba.

Ana zaton wuta a makera: An tsige DPO na 'yan sanda saboda zargin rashawa
Ana zaton wuta a makera: An tsige DPO na 'yan sanda saboda zargin rashawa

Sanarwan da ta fito daga bakin kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, Chike Oti ya ce an jawo hankalin kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Edgal Imohimi kan wata rahoton da wata jarida ta wallafa a ranar Juma'a mai taken "Wani DPO da karfin mulki ta rude shi ya jagoranci tawagarsa zuwa masallaci don kai samame."

DUBA WANNAN: 2019: Rikicin tikitin takarar shugabancin kasa ya raba kan masu ruwa da tsaki a PDP

Oti ya ce rahoton da hukumar 'yan sandan ta samu an ruwaito cewa DPO na caji Ofis din Pen Cinema a jihar Legas, Harrison Nwabusi da tawagarsa sun rika gudanar da samame suna karbar kudade daga hannun jama'a.

Ya ce an ruwaito cewa anyi samamen ne a ranar Laraba a layin Alimi Ogunyemi a unguwar Ifako Ijaiye kuma an bayyana cewa wani mutum mai suna Sherrif Aranjure yana daya daga cikin wadanda su shaida cewa DPO ya yi kwace a unguwar.

Hukumar 'yan sandan tana kira ga Sherrif Aranjure da duk wasu wanda suka shaida afkuwar lamarin su bayyana a ofishin mataimakin kwamishinan 'yan sanda sashin SCIID da ke Panti Yaba domin su taimaka wajen binciken.

Hukumar ta ce dukkan wadanda aka samu da hannu cikin aikata laifin za su fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel