Magori wasa kanka da kanka: Na fi Buhari mutunci da kima a idon duniya – inji dan takarar shugaban kasa

Magori wasa kanka da kanka: Na fi Buhari mutunci da kima a idon duniya – inji dan takarar shugaban kasa

Hamshakin attajiri, Datti Baba Ahmed wanda ya taba zama Sanatan yankin Zaria a karkashin jam’iyyar CPC ta baba Buhari yace ya duba kuma ya bincika, bai ga wani dan takarar shugaban kasa daya kai shi mutunci da kima ba, har da shubanan kasa Muhammadu Buhari.

Datti ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da jaridar Daily Trust, inda yace a duk tarihinsa babu inda ake kula da iyalinsa ko wasu hidindimunsa da kudin gwamnati, don haka shi yafi dacewa a zaba shugaban kasar Najeriya a karkashin inuwar PDP..

KU KARANTA: Kalli yadda mayakan Boko Haram suka gudanar da bikin Sallah a dokar daji

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shi yana bayyana wasu badakala da suka zubar da mutuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari a idon jama’a, inda yace daga ciki akwai bahallatsar kudaden hukumar kula da rarar man fetir,PTF, da Buhari ya rike a zamanin Abacha.

Magori wasa kanka da kanka: Na fi Buhari mutunci da kima a idon duniya – inji dan takarar shugaban kasa
Baba Ahmad

Haka zalika Datti yace sauran badakaloli da suka taba mutuncin Buhari akwai yadda aka tattara kudaden yakin neman zaben Buhari tun daga shekarar 2003, 2007, 2011 har zuwa 2015, yace shi kam bas hi da wannan tabon a tare dashi.

Daga karshe Datti yace shine kadai dan majalisa daya tilo daya tilo a cikin sama da yan majalisu dubu daya da suka yi aiki a majalisa a jamhuriyya ta hudu daya kirkiro dokar hana jami’an gwamnatin arigizon kwangilolin ayyukan gwamnati.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel