Sauyin sheka da harigido bai isa ya rikita ni ba - Shugaba Buhari

Sauyin sheka da harigido bai isa ya rikita ni ba - Shugaba Buhari

A yau Alhamis ne shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa duk wata harigido da masu sauya sheka da magoya bayansu ba zai dauke hankalinsa daga cigaba da yiwa jama'ar Najeriya ayyukan cigaba da yasa a gaba ba.

Shugaban kasa ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali ne wajen cikawa talakawa alkawuran da ta dauka a yayin yakin neman zaben shekarar 2015 wanda suka hada da habbaka tattalin arziki, samar da tsaro da kuma yaki da rashawa.

A jawabin da ya yi wajen walimar da ya yi tare da gwamnonin jam'iyyar APC da wasu 'yan majalisar tarayya a Daura da ke jihar Katsina, shugaban kasan ya jadada cewa APC ta fahimci matsalolin da ke adabar Najeriya kuma zata magance su tare da goyon bayan da jama'a ke bata.

Sauyin sheka da harigido bai isa ya rikita ni ba - Shugaba Buhari
Sauyin sheka da harigido bai isa ya rikita ni ba - Shugaba Buhari

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun dakile wani yunkurin kona coci a jihar arewa

A wata sanarwa da ta fito bakin mai taimakawa shugaban kasa a fanin yada labarai, Malam Garba Shehu, Shugaba Buhari ya ce, "Muna samun kwarin gwiwa duk lokacin da jama'ar mazabunmun ke murna da irin ayyukan da mu keyi kuma muna sane da alkawurran da muka dauke lokacin kamfe a 2015.

"Mun mayar da hankali sosai a fanin samar da tsaro, tattalin arziki da yaki da rashawa. Ko 'yan adawa baza su kushe irin kokarin da mu keyi wajen magance matsalolin Najeriya da muka ganoi ba.

"Zamu cigaba da gudanar da ayyukan da muka sanya a gaba a mulkinmu kuma muna godiya ga jama'ar mazabunmu saboda goyon bayan da suke bamu."

Da ya yi tsokaci kan batun sauya shekan 'yan siyasa, shugaba Buhari ya nanata maganar da ya yi a baya: "Muna fatan alheri ga dukkan wadanda suka sauya sheka zuwa wasu jam'iyyun."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel