Hajjin bana: An kama wani dan arewacin Najeriya a Saudiyya saboda dukan dan sanda
'Yan sanda a kasar Saudiyya sun kama wani Alhaji dan asalin jihar Adamawa dake arewacin Najeriya saboda dukan wani dan sanda da karfen rodi.
Jakadan Najeriya a kasar Saudiyya, Isa Dodo, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Mina dake Makkaah, ranar Laraba.
Dodo ya kara da cewa lamarin ya faru ne kwanan nan a Madina yayin da dan sandan dake bakin aiki ke kokarin shawo kan cunkuson jama’ar da suka ziyarci makabartar Bakiyya mai tarihi.
A cewar Dodo, dan Najeriyar ya harzuka tare da daukan wani karfen rodi da ya yi amfani da shi wajen dukan dan sandan a ka saboda ya ture shi bayan ya saba ka’idar bin layi a makabartar.
Dodo ya cigaba da cewa nan da nan jami’an ‘yan sanda suka cakume mutumin, da aka sakaye sunan sa, tare da tafiya da shi ofishinsu.
DUBA WANNAN: Bikin Sallah: Hotunan hawan daushe a jihar Kano
“Amma bayan jam’iar hukumar Alhazai ta kasa sun isa ofishin ‘yan sandan bayan samun labari, sai aka shaida masu an garzaya da alhajin, dan Najeria, zuwa asibitin mahaukata domin gudanar da yi masa gwajin hankali,” a cewar Dodo.
“Likitocin Saudiyyya sun tabbatar da cewar alhajin bashi da koshiyar hankali kuma nan take suka sake shi. Yanzu haka mun saka idanu a kan sa domin tabbatar da ganin bai maimaita irin wannan abu da ya yi ba a gaba,” in ji Dodo.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng