Uwargidan Najeriya ta tallafawa Mata 200 da kudin kafa sana’a

Uwargidan Najeriya ta tallafawa Mata 200 da kudin kafa sana’a

- Hajiya Aisha Buhari ta taimakawa wasu Matan kauyuka da jari

- Matar Shugaban kasar ta zabi Mata har 200 masu sana’a a Daura

- Bayan haka Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta bude wani ofis

Mun samu labari ba da dadewa ba cewa Matar Shugaban kasa Aisha Muhammadu Buhari ta fitar da dinbin mata daga cikin kunci a Arewacin Najeriya inda ta ba su kudi domin su samu jarin fara wani sana’a a Kasar.

Uwargidan Najeriya ta tallafawa Mata 200 da kudin kafa sana’a
Aisha Buhari ta tallafawa Mata 200 a Katsina Hoto: Aisha Buhari/Facebook

Uwargida Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta bayyana cewa a shirin da ta ke yi na inganta rayuwar mata a Najeriya, ta tallafawa wasu mata har 200 marasa karfi da jari domin su fara sana’ar da za ta rike su da iyalan su.

Matar Shugaban kasar tayi wannan gagarumin aiki ne a Garin Daura a Jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya. Mata 200 ne za su amfana da wannan taimako na Matar Shugaban kasa wanda ya fito daga Garin na Daura.

KU KARANTA: Tsohon Gwamna ya taimakawa wani maras karfi da jari

Uwargidan Najeriya ta tallafawa Mata 200 da kudin kafa sana’a
Aisha Buhari ta bude wani makeken ofis a Daura domin taimakon mata

Bugu da kari dai Uwargidan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kuma kafa wani katafaren ofishi domin irin wannan aiki a Garin na Daura. Matar Shugaban na Najeriya tana zabo matada ke cikin karkarori domin ta dafa masu.

Kafin a kafa Gwamnati dai Shugaban Kasar ya nuna cewa ba zai yi aiki da ofishin Uwargidar Shugaban kasa ba. Yanzu dai kusan ka iya cewa an dawo da ofishin na Matar Shugaban kasa ta bayan fage domin taimakawa mata.

Kwanaki kun ji cewa Aisha Buhari ta zama Jakadar musamman ta Majalisar Dinkin Duniya kan cutar kanjamau a Najeriya. Matar Shugaban kasar za tayi bakin kokari wajen ganin an rage kamuwa da cutar nan ta sida mai illa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel