Yadda Sanata Wammako ya azurta wani mai sana’ar sayar da Kwakwa a ranar Sallah

Yadda Sanata Wammako ya azurta wani mai sana’ar sayar da Kwakwa a ranar Sallah

Allah ya tarfa ma garin wani mai sana’aor sayar da Kwakwa nono a lokacin da yayi arangama da wani tsohon gwamnan jihar Sakkwato kuma, Sanata a majalisar dattawa, Aliyu Magatakarda Wammako.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Sallah, a loakcin da Wammako ke zaune a wajen da ake yanka masa dabbobinsa bayan ya sauko daga Sallar Idi, kwatsam sai ga wannan mutumi mai sayar da Kwakwa yana talla, ‘A sayi kwakwa mai dadi.”

KU KARANTA: Atiku ya mayar da martani game da tattakin mita 800 da Buhari yayi a garin Daura

Yadda Sanata Wammako ya azurta wani mai sana’ar sayar da Kwakwa a ranar Sallah
Sanata Wammako

Jin haka Sanata ya kira mai kwakwa, inda ya tambayeshi nawa ne kudin kwakwar dake kan baron nasa gaba daya, sai mai kwakwa yace “Yallabai dubu hudu ne gaba daya.” Ya tsaya yana tsimayin abinda zai faru.

Nan take Sanata ya sanya hannu a cikin aljihu, ya dumbuzo kudin da Allah ne kadai ya san adadinsu, ya damka ma wanann bawan Allah da nufin ya biya shi kudin kwakwarsa gaba daya, sa’annan yace ma jama’a kowa ya dibi Kwakwa son ransa.

Yadda Sanata Wammako ya azurta wani mai sana’ar sayar da Kwakwa a ranar Sallah
Sanata Wammako

Ganin haka mai kwakwa ya rasa abinda zai ce, kawai sai ya fashe da kukan murna yana godiya ga Wammako, daga nan ya tattara inasa inasa ta wuce gida yana cikin halin tsananin farin ciki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel