Babban hafsan Sojan sama ya ziyarci Sojojin dake bakin daga don gudanar da bikin Sallah

Babban hafsan Sojan sama ya ziyarci Sojojin dake bakin daga don gudanar da bikin Sallah

Babban hafsan rundunar mayakan Sojan sama, Sadique Abubakar ya kai ma Sojojin dake bakin daga ziyara a garuruwan Miaduguri da Yola inda ya gaba ta manya da kananan Sojoji tare da jinjina ma kokarin da suke yi don samar da tsaro.

Legit.ng ta ruwaito Abubakar ya saba kai ma Sojoji ziyara a yayin bukuuwan Sallah, hakan ne ya sanya shi a wannan karon zuwa garin Yola, inda kaddamar da wasu sabbin dakuna dai dai guda 24 da ya gina ma hafsoshin Sojojin da basu da aure.

KU KARANTA: Atiku ya mayar da martani game da tattakin mita 800 da Buhari yayi a garin Daura

Babban hafsan Sojan sama ya ziyarci Sojojin dake bakin daga don gudanar da bikin Sallah
Babban hafsan Sojan sama

Sa’annan ya kaddamar da wani wajen nishadi da hutawa na Sojoji a Asibitin Sojan sama dake garin Yola, inda yace an samar da abubuwan ne don tabbatar da jin dadi tare da walwalar Sojojin sama, don kara musu kaimi wajen gudanar da ayyukansu.

Bugu da kari, Abubakar yay aba da kokarin da Sojoji sama dake garin Yola suke yi wajen kai farmaki ga duk wani sansanin yan ta’adda dake jihar Adamawa gaba daya, inda yace sun yi kyawun kai, sa’annan ya shawarcesu da su guji shiga siyasa, ba nasu bane.

Babban hafsan Sojan sama ya ziyarci Sojojin dake bakin daga don gudanar da bikin Sallah
Dakunan

Daga karshe Abubakar ya bayyana godiyar rundunar Sojan sama gaba daya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa goyon bayan da yake baiwa rundunar, musamman ta bangare samar da matsugunnai, da kuma walwalar jami’anta.

Shima a nasa jawabin, Kwamanda James Gwani ya yaba ma shugabansu da ziyarar daya kai musu, inda yace a duk lokacin da ya kai ma Sojojin dake bakin daga ziyara, suna samun gagarumar kwarin gwiwa.

Babban hafsan Sojan sama ya ziyarci Sojojin dake bakin daga don gudanar da bikin Sallah
Babban hafsan Sojan sama

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel