Muhimman wuraren nishadantarwa guda 5 daya kamata masoya su kai ziyara a jihar Kano

Muhimman wuraren nishadantarwa guda 5 daya kamata masoya su kai ziyara a jihar Kano

Sallah bikin rana daya, inji Malam Bahaushe, sai dai jama’a na amfani da wannan lokaci na farin ciki wajen bayyana murnarsu, tare da shiga cikin duk wani shagali da zai kawo nishadanatarwa da annushuwa, duk don ganin an ci moriyar lokacin yadda ya kamata.

Legit.ng ta kawo muku wasu muhimman wuraren samun nishadi guda biyar a jihar Kano, inda masoya, iyali ko kuma yan yawon Sallah zasu je a cikin shagulgulan Sallah, daga cikin wuraren nan akwai:

KU KARANTA: Dakaraun Sojin Najeriya sun yi ma mayakan Boko Haram kisan kiyashi a wata arangama

Hawan Sallah

Ana yin hawan Sallah a jihar Kano a duk shekara a yayin karamar Sallah da babbar Sallah, inda mahaya dawakai suke taka ma Sarki baya, daga cikin hawan da ake yi a Kano akwai hawan Sallah, hawan Daushe, hawan Nasarawa, hawan Panisau, Hawan Dorayi.

Muhimman wuraren nishadantarwa guda 5 daya kamata masoya su kai ziyara a jihar Kano
Hawa a Kano

Tiga Dam

Akwai wani babbar madatsar ruwa dake garin Tiga na jihar Kano, inda jama’a ke zuwa don nishadantarwa, ana hawan kwale kwalen zamani a cikin tafkin Tiga, Tiga Dam yayi daidai ga masoya.

Minjibir Park

Shima wani matattarar yan birni ne dake garin Minjibir na jihar Kano, wanda ya kunshi kayan wasanni da dama don amfanin kananan yara, da kuma kwamin ruwa wanda aka fi sani da ‘Swimmin Pool’, zaka ji dadin wurin idan ka je.

Gidan Zoo

Gidan ajiyan dabbobi dake cikin birnin Kano wani wuri ne dake samun baki da dama daga ciki da wajen Kano a yayin bukukuwan Sallah, inda jama’a ke kai ziyara don gane ma idanuwansu irin dabbobin dake ajiye a wannan gida, daga cikinsu akwai Zaki, Giwa, Macizai, Birai, Jimina, kunkuru da sauransu.

Muhimman wuraren nishadantarwa guda 5 daya kamata masoya su kai ziyara a jihar Kano
Gidan zoo

Ada Bayero Mall

Rukunin shaguna na Ado Bayero na nan akan titin gidan Zoo dake cikin birnin Kano, wanda ya kunshi manyan katafaran shaguna, daga cikinsu akwai wajen saye saye mai suna Shoprite, akwai wajen buga wasannin zamani Games, akwai gidan kallon fina finai da sauransu

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel