Buhari ya yi tafiya da ƙafafunsa ta tsawon mita 800 bayan halatar Sallar Idi a garin Daura

Buhari ya yi tafiya da ƙafafunsa ta tsawon mita 800 bayan halatar Sallar Idi a garin Daura

A yau Talata da take ranar babbar Sallah ga dukkanin Musulmai na duniya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci Sallar Idi ta raka'o'i biyu tare da dubunnan Musulmai a mahaifar sa ta garin Daura dake jihar Katsina a arewacin Kasar nan.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, shugaban kasa Buhari ya isa filin Sallar Idi da misalin karfe 9.48 a safiyar yau ta Talata tare da hadimai gami da yan uwan sa.

Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaba Buhari ya kuma yanka ragon sa na layya bayan gudanar da sallar sa ta Idi a garin na Daura.

Shugaba Buhari yayin tattaki bayan halartar Sallar Idi a garin Daura
Shugaba Buhari yayin tattaki bayan halartar Sallar Idi a garin Daura

Wani rahoto mai cike ta ban mamaki da shafin jaridar Daily Trust ta ruwaito ya bayyana cewa, shugaban kasar ya kuma yi tattaki da sawayen sa har na fiye da tsawon mita 800 daga filin idin har zuwa gidan sa, inda daruruwan masoya ke ma sa kururuwa da waƙe na 'Sai Baba'.

KARANTA KUMA: 2019: Ina da duk wata cancanta ta ƙalubalantar Shugaba Buhari - Tambuwal

Cikin huduba ta babban Limamin garin Daura, Safiyanu Dansanwai, ya yi kira kan zaman lafiya a kasar nan tare da neman al'umma kan hada kawunan su wajen tabbatar da ci gaban kasar.

Kazalika Sarkin Daura, Alhaji Farouk Umar, yana daya daga cikin dubunnan al'ummar da suka halarci Sallar Idin tare da shugaban kasa Buhari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel