An yiwa Gwamna El-Rufa'i sarauta
Rahotannin da muka samu daga bakin gwamnatin jihar Kaduna ta ce an yiwa gwamna Nasir El-Rufai na jihar sarautar Garkuwan Talakawa.
Sakon ya fito ne daga shafin Twitter na gwamnatin jihar inda ta ce Masarautar Jama'a ce ta yiwa El-Rufai wannan nadin sarautar bayan ya yi sallar Idi a garin Kafanchan kamar yadda BBC ta wallafa.
Ma'abota dandalin Twitter dake bibiyar shafin gwamnatin sun tofa albarcin bakinsu a kan nadin sarautar inda su kayi kira a gareshi ya yi amfani da damar da ya samu domin aiwatar da ayyukan da zasu kawo cigaba ga talakawan jihar.

"Ina taya ka farin ciki. Ina kuma addu'a da fatan gannin wannan mukami da aka ba ka ya zame maka kaimi wurin aiwatar da shirye-shiryen da zasu inganta rayuwar talakwa," inji Dr. Tim Zakwai Auta.
DUBA WANNAN: Bikin Sallah: Gwamna Tambuwal ya yiwa marayun Sakkwato sha tara na arziki

Gwamna El-Rufai ya kasance mutum ne mai dogewa kan aiwatar da manufofin da ya sanya a gaba ko da wasu lokutan jama'a na ganin manufofin sun saba tunanin talakawa.
Wasu daga cikin sun hada da rushe gine-gine, sallamar malaman makarantun firamare da sakandare da tsige wasu masu rike da sarautun gargajiya sai dai gwamnan ya sha nanatawa cewa dukkan matakan da ya ke dauka na kawo gyara ne.

Daga baya gwamnan ya dauki sabbin malaman makaranta bayan anyi musu jarabawa tare da tantancesu, ya kuma dukufa wajen gyaran tituna da gyaran kwalbati a wurare da yawa a jihar.
Gwaman kuma ya kaddamar da shirin bayar da ilimi kyauta a jihar tare da ciyar da daliban firamare da ma wasu ayyukan more rayuwa da dama.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng