Sakon Buhari na sallah: Fasa yaki da cin hanci cin amanar mutanen Najeriya ne

Sakon Buhari na sallah: Fasa yaki da cin hanci cin amanar mutanen Najeriya ne

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar hakura da yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatinsa ke yi zai zama cin amana ga ‘yan Najeriya duk hakan ya jawo masa Karin makiya.

Shugaba Buhari na wadannan kalamai ne a sakonsa na Sallah babba ga musulmin Najeriya mai dauke da sa hannun Malam Garba Shehu, mai taimakawa shugaban na musamman kan yada labarai.

Buhari ya bayyana nadama da damuwar sa bias yadda ya ce jama’a sun yi watsi da koyar wa irinta addini tare da bawa son zuciya fifiko.

Sakon Buhari na sallah: Fasa yaki da cin hanci cin amanar mutanen Najeriya ne
Buhari

A sakon, Buhari ya bayyana cewar kamata ya yi mutane su yi amfani da tasirin addini wajen inganta halaye da dabi’un su kamar yadda addinai suka bawa hali nigari muhimmanci.

DUBA WANNAN: Bikin Sallah: Gwamnatin jihar Kaduna ta rufe wuraren shakatawa

Ba zan hakura da yaki da cin hanci da rashawa ba, yin hakan tamkar cin amanar ‘yan Najeriya ne. Cin hanci da rashawa na lalata kasa da cigaban al’umma a sabode b azan fasa yaki wannan mummunar dabi’a ba duk da haka ta jawo min Karin makiya,” a cewar shugaba Buhari.

Kazalika ya bukaci ‘yan Najeriya su zama mau hakuri da son juna domin taimakon gwamnati a kokarinta na samar da zaman lafiya mai dorewa a fadin kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel