Hari la yau: ‘Yan bindiga sun sace matar malamin addini bayan sun kashe shi

Hari la yau: ‘Yan bindiga sun sace matar malamin addini bayan sun kashe shi

Wasu masu garkuwa da mutane sun kashe Hosea Akuchi, babban fasto a Cocin Baptist dake Guguwa a garin Nasira dake karkashin karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Masu garkuwar sun kashe Fasto Akuchi ne bayan ya ki yarda su tafi da shi yayin da suka kai masa hari a jiya, Lahadi. Sai dai duk da haka masu garkuwa da mutanen sun sace matar sa, Talatu.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewar ‘yan bindigar sun isa garin da misalign karfe 1:00 na dare tare da yin harbin iska kafin daga bisani su bankara kofa su shiga gidan Faston.

Hari la yau: ‘Yan bindiga sun sace matar malamin addini bayan sun kashe shi
‘Yan bindiga sun sace matar malamin addini bayan sun kashe shi

Yakubu Sabo, kakakin hukumar ‘yan sanda a jihar Kaduna, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da sanar da cewar malamin addinin ya rasa ran sa yayin da yake kokarin tirjewa ‘yan bindigar dake son sace shi.

“Sun harbe shi ne bayan sun ga ba zai tafi tare da su cikin sauki ba,” a cewar Sabo.

DUBA WANNAN: Al-Mustapha ya yi tone-tone a kan kungiyar Boko Haram

Sannan ya kara da cewa, “mun ziyarci gidansa, inda abin ya faru, kuma muna iya bakin kokarinmu domin bankado ko su waye suka aikata wannan ta’addanci.

Sabo ya bayyana cewar hukumar ‘yan sanda na iya bakin kokarinta domin tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar Kaduna duk da wasu batagari na cigaba da kawo tarnaki ga kokarinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel