Alkalumman tarin dukiya da rayukan jama’a da aka yi asara sakamakon rikicin jihar Zamfara

Alkalumman tarin dukiya da rayukan jama’a da aka yi asara sakamakon rikicin jihar Zamfara

Sakamakon matsalar tsaro da ta dabaibaye jihar Zamfara, musamman hare haren yan bindiga dadi, kiyasi ya nuna akalla mutane dubu uku ne suka rasa ransu, tare da asarar dukiya ta naira biliyan goma sha bakwai lamarin ya haifar.

DailY Trust ta ruwaito sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Abdullahi Shinkafi ne ya sanar da haka a ranar Lahadi, 19 ga watan Agusta, a yayin wani taron ganawa da jama’a da kungiyar lauyoyin jihar ta shirya, inda yace an sami wadannan alkalumman ne a cikin shekaru bakwai da suka gabata.

KU KARANTA: Abinda shugaba Buhari yake nufi da ‘cigaba da kama barayi’ – Kaakakin gwamnati

Shinkafi yace sama da mutane dubu uku ne suka mutu a sakamakon hare haren, yayin da gidaje dubu biyu suka salwanta, anyi asarar motoci dari biyar, sa’annan an sace sama da mutum dari biyar don neman kudin fansa.

Alkalumman tarin dukiya da rayukan jama’a da aka yi asara sakamakon rikicin jihar Zamfara
Yan gudun hijira sakamakon rikicin jihar Zamfara

s

“Mun kashe naira biliyan 17 wajen yaki da yan bindigan, idan wani yaji biliyan 17 sai a dauka wani uban kudi ne, amma idan aka farfasa maka shi, zaka san bai ma isa ba, a shekarar 2011 mun saya ma hukumomin tsaro motocin aiki guda 457.

“A 2012 mun saya musu motoci 2,250, a shekarar 2014, mun saya musu guda 77, sa’annan a shekarar 2015, 2016., 2017 da 2018 mun saya musu motoci hamsin hamsin. Haka zalika mun bibbiya kudaden tallafi ga mutanen da hare haren ya shafa.” Inji shi.

Farfesa Shinkafi ya koka game da matsanancin matsalar da ake fuskanta a jihar, don haka yayi kira ga jama’a da ma gwamnatin tarayya da su taimaka wajen lalubo hanyoyin shawo kan matsalar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel