Shugaban marasa rinjaye na majalisar jihar Gombe ya sauya sheka zuwa PDP

Shugaban marasa rinjaye na majalisar jihar Gombe ya sauya sheka zuwa PDP

Shuagaban marasa rinjaye na jam'iyyar APC a majalisar jihar Gombe, Alhaji Usman Haruna ya sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar ne a yayin zaman majalisar da Kakakin majalisar, Alhaji Nasiru Abubakar Nono ya jagoranta a jiyar Alhamis.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar jihar Gombe ya sauya sheka zuwa PDP
Shugaban marasa rinjaye na majalisar jihar Gombe ya sauya sheka zuwa PDP

DUBA WANNAN: Matar aure ta mutu a dakin saurayinta bayan ta gama cin amanar mijinta

Haruna ya ce ya fice daga jam'iyyar APC ne saboda rashin rikicin da ya barke a jam'iyyar APC reshen jihar Gombe da kuma irin rashin adalcin da shugabaninn jam'iyyar suka masa.

Ya kara da cewa, watanni hudu da suka gabata, jam'iyyar ta dakatar dashi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba wanda hakan rashin adalci ne a ganinsa.

Ku biyo mu domin karin bayani...

Asali: Legit.ng

Online view pixel