Yaushe Shugaba Buhari zai dawo gida Najeriya?
Fadar shugaban kasar Najeriya ranar Asabar dinnan shugaba Buhari zai dawo gida Najeriya, bayan ya kammala hutun da ya dauka na aiki
Fadar shugaban kasar Najeriya ranar Asabar dinnan shugaba Buhari zai dawo gida Najeriya, bayan ya kammala hutun da ya dauka na aiki.
Shugaban kasar ya tafi birnin Landan domin hutun kwanaki goma, wanda ya fara a ranar 3 ga watan Agustan nan. A farkon wannan satin ne wasu jaridun Najeriya suka dinga yada jita - jitar cewa shugaban kasar ya dage ranar dawowar tashi, inda suke nuna cewa zai wuce kwanaki goman da ya dauka.
DUBA WANNAN: Ko kun san a nawa jam'iyyar PDP ke sayen katin zaben jama'a a jihar Yobe?
To sai dai kuma fadar shugaban kasa ta musanta jita - jitar da jaridun ke yadawa.
Mai magana da yawun shugaban kasa a fannin yada labarai, Malam Garba Shehu ya shaidawa manema labarai cewa a ranar Asabar dinnan shugaban kasar zai dawo gida Najeriya.
Malam Garba Shehu ya bayyana cewa shugaba Buhari zai yi kwanaki goma ne kamar yanda aka tsara, don haka baza a saka ranar Asabar da Lahadi a cikin lissafi ba, domin suna cikin karshen mako, wanda ba lokacin aiki bane, lokaci ne na hutu.
A shekarar da ta gabata dai shugaba Buhari ya shafe watanni yana hutu a birnin na Landan, abin da ya kawo ce-ce-ku-ce a kasar nan.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng