Ko kun san a nawa jam'iyyar PDP ke sayen katin zaben jama'a a jihar Yobe?

Ko kun san a nawa jam'iyyar PDP ke sayen katin zaben jama'a a jihar Yobe?

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar Yobe, Alhaji Adamu Chilariye ya zargi jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da sayen katin zaben al'umma

Ko kun san a nawa jam'iyyar PDP ke sayen katin zaben jama'a a jihar Yobe?
Ko kun san a nawa jam'iyyar PDP ke sayen katin zaben jama'a a jihar Yobe?
Asali: Depositphotos

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar Yobe, Alhaji Adamu Chilariye ya zargi jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da sayen katin zaben al'umma.

Yayi wannan zargin ne a jiha Alhamis a wata tattaunawa da yayi da manema labarai. Ya bayyana cewa an sanar da manyan jam'iyyar APC na jihar irin ta'asar da jam'iyyar PDP din take.

DUBA WANNAN: Kuji irin maganganu masu ratsa zuciya da Nafisa Abdullahi ta dinga yi akan gawar mahaifiyarta

"Manyan shugabannin jam'iyyar PDP na jihar Yobe suna amfani da damar su suna sayen katin zaben jama'a akan kudi naira 5,000 duk guda daya." Ya ce jam'iyyar APC ta kai korafi akan ta'asar da jam'iyyar PDP din take ga hukumar tsaro.

Bayan haka, Chilariye ya shawarci jama'a da su lura dakyau kada suje su fada tarkon jam'iyyar PDP.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel