Kano ta dabo tumbin giwa: Buhari da Ganduje zasu samar da bahaya miliyan 20 a jihar Kano

Kano ta dabo tumbin giwa: Buhari da Ganduje zasu samar da bahaya miliyan 20 a jihar Kano

Wani aikin hadaka tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Kano zai samar da sabbin bahaya guda miliyan ashiri da dubu dari shidda (20,600,000) a jihar Kano don taimaka ma kokarin gwamnati na tabbatar da tsafta da kuma rage yaduwar cututtuka.

Jaridar Premium Times ta ruwaito gwamnatocin biyu sun tabbatar da wannan shiri ne yayin bikin rattafa hannu akan yarjejeniyar samar da taftataccen ruwan sha tare da kuma tabbatar da tsaftar muhalli a jihar Kano.

KU KARANTA: An sake kwatawa: Kwastam ta kama wani babban sunduki da ya shigo Najeriya makare da kakin Sojoji

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ministan ruwa, Suleiman Adamu ne ya bayyana haka a garin Abuja a ranar Alhamis, 16 ga watan Agusta, inda yace wannan aiki ya kunshi gyarana famfuna da rijiyoyi burtsatsi guda dubu saba’in da sittin da casa’in da uku (77,693) tare da gina sabbi guda dubu goma sha bakwai da dari biyu da sittin da hudu (17,264).

Kano ta dabo tunbim giwa: Buhari da Ganduje zasu samar da bahaya miliyan 20 a jihar Kano
Dakin bahaya

Minista Suleiman yace wannan aiki zai lakume kimanin naira biliyan goma sha biyu da miliyan dari bakwai (N12.1bn), wanda gwamnatocin biyu zasu hada, kuma za’a kwashe shekaru goma sha biyar ana gudanar da aikin.

Haka zalika Minista yace daga shekarar 2019 zuwa shekarar 2025, ana sa ran gina dakunan bahaya guda miliyan ashirin da dubu dari shida a jihar Kano, don hana jama’a yin bahaya akan hanyoyi da tituna wanda hakan ke sabbaba yaduwar cututtuka.

Shima gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje yayi maraba da wannan aiki, inda yace manufar aikin shine samar da ingantaccen rayuwa ga jama’an jihar Kano, ya kara da cewa a kasafin kudin bana ya sanya naira biliyan 32 don samar da tsatataccen ruwan sha.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel