Kotu ta tursasa wani mutum ya dinga biyan tsohuwar matarsa 12,000 duk wata

Kotu ta tursasa wani mutum ya dinga biyan tsohuwar matarsa 12,000 duk wata

- Wata kotu ta umarci tsohon mijin wata mata daya dunga bata kudin abinci duk wata

- Matar dai ta maka mijin nata a kotu ne akan ya saketa tana dauke da cikin sa

- Ya bayyana wa kotu cewa zai dunga bata N6,000 a wata inda kotu tace yayi kadan

Kotu ta tursasa wani mutum ya dinga biyan tsohuwar matarsa 12,000 duk wata
Kotu ta tursasa wani mutum ya dinga biyan tsohuwar matarsa 12,000 duk wata

A ranar Alhamis ne wata kotu dake zamanta Magajin gari Kaduna, ta umarci wani mai suna Alhassan Abdullahi daya dunga bawa tsohuwar matarsa Zainab Shuaibu kudin abinci N12,000 duk wata.

Shuaibu ta maka tsohon mijin nata a kotu ne inda take cewa mijin nata ya saketa ne a makwanni Biyu da suka gabata bayan tana dauke da ciki da jariri dan watanni Bakwai.

DUBA WANNAN: An nemi makiyaya dasu daina tada zaune tsaye

"Ya sake ni bayan yasan cewa ina dauke da cikin sa na watanni Uku" saboda haka nake rokon wannan kotu data sanya tsohon mijina ya nema mana wajen zama da kuma kudin abinci.

Abdullahi ya cewa kotu zai nema mata wajen zama da kuma kudin abinci N6,000 a duk wata.

Alkalin kotun Dahiru Lawan yace N6,000 tayi kadan inda ya umarce shi daya dunga bawa Zaiban N12,000 a duk wata.

Sannan kotu ta umarci Zainab da ta koma muhallin da tsohon mijin nata ya samar mata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel