Kayi tsufa da mulkin Najeriya - Tambuwal ya fadawa Buhari

Kayi tsufa da mulkin Najeriya - Tambuwal ya fadawa Buhari

Gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ce shugaba Muhammadu Buhari mutumin kirki ne kuma yana da nagarta amma tsufa na kawo masa cikas wajen gudanar da ayyukansa a matsayinsa na shugaban kasa.

A yayin da yake jawabi da dandazon kungiyoyin matasa da dalibai da suka kai masa ziyarar ban girma a jiya Laraba a Sakkwato, Tambuwal ya amince da cewa matsin lambar da ake masa na fitowa takarar shugabancin kasa ta fara yawa.

Sai dai gwamna Tambuwal ya musanta zargin da ake masa na cewa yana daya daga cikin makiyan shugaba Muhammadu Buhari.

Ka hakura da mulki ka bar wa matasa - Tambuwal ya fadawa Buhari
Ka hakura da mulki ka bar wa matasa - Tambuwal ya fadawa Buhari

DUBA WANNAN: An matsa min lamba na fito takarar shugaban kasa - Gwamna Tambuwal

"Muna kaunan shugaba Buhari shi yasa muka goyi bayansa a shekarar 2015, kuma ko wancan lokacin mun san cewa zai nemi yin tazarce sai dai idan abubuwa basu tafiya yadda ya kamata, ya zama dole mu sanar dashi.

"Mun amince da nagartarsa, kishin kasa da kuma jarumtarsa amma wadandan halaye kawai ba sune ke tabbatar da cancantar shugaba ba.

"Dukkan mu mun san cewa akwai wata gibi a gwamnatin nan saboda rashin lafiyarsa ko kuma nisan shekarunsa. Hakan yasa 'yan Najeriya ke bukatar shugabani masu karancin shekaru da zasu jagorance su," inji shi.

Gwamna Tambuwal ya yi ikirarin cewa akwai wasu tsirarun mutane a gwamnatin Buhari ta su kayi kane-kane kuma su ka juya gwamnati yadda suke so ba shugaba Buhari ba.

A cewarsa, Najeriya na bukatar shugaba da zai rika biyaya ga dokar kasa kuma wanda ba zai nuna banbanci ba wajen yaki da rashawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel