Bikin Sallah: Gwamnonin Arewa 5 da suka biya ma’aikata albashi kafin Sallah

Bikin Sallah: Gwamnonin Arewa 5 da suka biya ma’aikata albashi kafin Sallah

Aka ce Sallah biki daya rana, idan kuma ta wuce sai ace Sallah ta wuce ta bar wawa da bashi, a kokarinsu na rangwanta ma ma’aikatan jihohinsu, wasu gwamnoni guda biyar sun ciri tuta ta hanyar biyan ma’aikatan nasu albashin watan Agusta.

Wadannan gwamnoni wanda dukkaninsu daga yankin Arewacin Najeriya suka fito sun biya ilahirin ma’aikatansu albashin watan Agusta ne tun kafin karshen wata, don su yi bikin Sallah da zai kama a ranar 23 cikin jin dadi da walwala.

KU KARANTA: Aiki har gida: Shugaba Buhari ya kammala shirin yi ma Atibu Abubakar sha tara ta arziki

Legit.ng ta ruwaito daga cikin gwamnonin akwai Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, Gwamna Abdulfatah Ahmad na jihar Kwara sai kuma Gwamnan jihar Yobe Ibrahim Gaidam.

Sauran gwamnonin da suka amince a biya ma’aikatan jihohinsu albashi sun hada da gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da kuma gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Atiku Bagudu.

Sai dai a wani hannun kuma, ma’aikata kan ji jiki idan gwamnati ta biyasu albashin gaba daya kafin karshen wata, saboda ba zasu sake jin kararrawa ba har sai karshen wata mai kamawa, akalla kwanak 40 kenan babu albashi sai dai wasu jihohin sukan biya rabin albashi, inda suke fanshewa daga albashin ma’aikatan a cikin watanni biyu zuwa uku.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel