Asha: 'Yan bindiga sun kashe tsohon mataimakin shuganban NPS a gonarsa
Hukumar kula da gidajen yari na kasa (NPS) ta tabbatar da rasuwar tsohon mataimakin shugaban hukumar, Nanvyet Gwali.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Francis Enobore, ne ya tabbatar da rasuwar Gwali a wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata a Abuja.
Enobore yace wasu 'yan bindigan da har yanzu ba'a san ko su wanene ba suka kashe Gwali a gonarsa da ke Laminga kusa da Keffi a jihar Nasarawa a ranar 10 ga watan Augusta.
DUBA WANNAN: Mata biyar da suka fi shahara a duniya
Marigayin ya baro aikinsa daga ma'aikatan ilimi na jihar Filato a shekarar 1989 ya fara a aiki a matsayin Superintendent a hukumar gidajen yari har ya kai matsayin mataimakin shugaban hukumar.
Ya yi murabus a watan Fabrairun 2016 a matsayin mataimakin shugaban hukumar mai kula da kudade da asusun ajiya.
Enobore yace hukumar ta tuntubi sauran hukumomin tsaro wanda ke bincike kan lamarin don ganin cewa wanda suka aikata wannan mummunan aiki sun fuskanci shari'a.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng