Za a karrama gwamnonin Najeriya da suka fi yiwa jama’a aiki, duba bangaren da kowanne yafi dagewa
Bayan kammala kada wata kuri’a a kan gwamnonin da suka fi yiwa jama’ar su aiyuka, za a karrama wasu gwamnonin Najeriya a wani taro na kasa da kasa da za a yi a birnin New York na kasar Amurka.
Gwamnan jihar Lagos, Akinwunmi Ambode, ne ya zo na farko a sahun gwamnonin da suka fi yiwa jama’ar su aiki kamar yadda wata jaridar nahiyar Afrika dake auna kwazon shugabanni duk shekara ta tabbatar.
Ragowar gwamnonin da bangarorin da suka samu yabo sun hada da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas a matsayin wanda ya fi shimfida aiyukan raya kasa da gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a matsayin wanda wanda ya fi shimfida aiyukan raya karkara.
Akwai Ibrahim Hassan Dankwambo na jihar Gombe a matsayin gwamnan da ya fi taka rawa a bangaren tsaro da tabbatar da zaman lafiya, Malam Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna a matsayin gwamnan da ya fi raya bangaren ilimi sai kuma hukumar kula harkokin sadarwa ta kasa (NCC) a matsayin hukumar gwamnati da ta zarce ragowar ta fuskar yin aikinta.
DUBA WANNAN: Jerin sunayen sanatocin APC 57 da jihohin su
Dakta Ken Giami, babban editan jaridar ne ya sanar da wannan sakamako a yau, Talata, bayan rufe dukkan cibiyoyin kada kuri’a ga gwamnonin.
Za a karrama gwamnoni da lambobin yabo a gaban fiye da mutane 300 ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa da jakadu da wakilan majalisar dinkin duniya a birnin New York ranar 25 ga watan gobe, Satumba, na shekarar da muke ciki, 2018.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng