Ambaliyar ruwa ta tagayyara mutane, ta lalata gidaje fiye da 50 a jihar Kebbi

Ambaliyar ruwa ta tagayyara mutane, ta lalata gidaje fiye da 50 a jihar Kebbi

A kalla gidaje 50 ne suka lalace sakamakon ruwan sama kamae da bakin kwarya da akayi a kauyen Dakingari dake karamar hukumar Suru na jihar Kebbi a daren jiya Litinin kamar yadda Punch ta wallafa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa ruwan daren ya yi sanadiyyar mutane da dama sun rasa muhallinsu a kauyen.

Direktan hukumar Agajin gagawa na jihar, Alhaji Rabiu Kamba, ya shaidawa NAN a birnin Kebbi a ranar Talata cewa har yanzu babu wanda ya rasa rayyursa sakamakon ambaliyar ruwan.

Mumunar ambaliyar ruwa ta lalata sama da gidaje 50 a Kebbi
Mumunar ambaliyar ruwa ta lalata sama da gidaje 50 a Kebbi

DUBA WANNAN: Gwamnatin Kano ta gano wasu mukuden daloli da Kwankwaso ya boye a Ukraine

"Har yanzu, bamu samu rahoton rasuwa ba sai dai sama da gidaje 50 sun lalace sakamakon ambaliyar ruwa da ta faru cikin dare," inji shi.

A cewar Kamba, jami'an hukumar bayar da agajin sun ziyarci wuraren da ambaliyar ta shafa domin kiyasta barnar da ambaliyar tayi.

"Muna tattara bayanai kan irin asarar da al'umma su kayi domin mu kaiwa gwamnati rahoto saboda a san irin tallafin da za'a bawa wadanda abin ya shafi," inji shi.

Kamba ya gargadi mazauni kauyen su guji amfani da ruwan rijiyarsu saboda ambaliyar ruwan ya gurabata ruwan rijiyoyin a yanzu.

"Zamu gaggauta kaiwa ma'aikatan lafiya na jiha rahoton bayanan da muka tattaro saboda a dauki matakan da suka dace," inji Kamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164