Sojin saman Najeriya sun ragargaji 'yan ta'adda a Zamfara, sun kashe da dama

Sojin saman Najeriya sun ragargaji 'yan ta'adda a Zamfara, sun kashe da dama

Dakarun rundunar sojin sama ta Najeriya dake yaki da aiyukan ta'addanci a jihar Zamfara karkashin Ofireshon Diran Mikiya ta kaddamar da wasu hare-hare a kan 'yan ta'adda a jejin Sububu, Birnin Magaji da Rugu.

Hare-haren na zuwa ne a lokacin da ayarin tawagar soji daban-daban ke taka rawa wajen kakkabe 'yan ta'addar da suka addabi jihar ta Zamfara.

A sanarwar da hukumar sojin sama ta fitar ta bakin Ibikunle Daramola, jami'in hulda da jama'a, ta bayyana cewar ta samu nasarar hallaka 'yan ta'addar da dama a jerin wasu hare-hare da ta kaddamar tsakanin 9 zuwa 11 ga wata a dazukan Birnin Magaji, Sububu, da Rugu dake jihar.

Sojin saman Najeriya sun ragargaji 'yan ta'adda a Zamfara, sun kashe da dama
Sojin saman Najeriya

Dakarun sojin sun kai hari dajin Sububu a ranar 9 ga watan Agusta bayan gano wata mafakar 'yan ta'adda. Hukumar ta ce 'yan ta'addar da yawa sun hallaka, sai dai ba ta ambaci adadi ba.

Kazalika hukumar ta bayyana cewar dakarun ta sun kai wani harin a dajin Birnin Magaji ranar 10 ga wata bayan gano wasu 'yan bindiga a kan Babura yayin wani sintiri ta jirgin sama mai saukar ungulu.

DUBA WANNAN: Saraki da Ikweremadu basu fi karfin kamu ko dauri ba - APC

Haka ma a ranar 11 ga wata dakarun sojin saman sun kai wani harin kan 'yan ta'addar a dajin Rugu. Sun kai harin ne bayan samun sahihan bayanai kan cewar 'yan ta'addar na amfani da dajin domin safarar makaman da suke amfani da su.

Sojojin sun hangi 'yan ta'adda da dama a kan Babura dauke da bindigu yayin da suka isa dajin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel