Mayakan rundunar Sojan kasa sun yi bore, sun kulle filin sauka da tashin jirage na Maiduguri

Mayakan rundunar Sojan kasa sun yi bore, sun kulle filin sauka da tashin jirage na Maiduguri

Hankula sun tashi, kuma jama’a sun shiga firgici a lokacin da wasu dakaru, kuma mayakan rundunar Sojan kasa ta Najeriya suka bude wuta a filin sauka da tashin jirage dake garin Maiduguri na jihar Borno, kamar yadda jaridar The Cables ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sojojin sun yi wannan bore ne sakamakon sauyin wajen aiki da shuwagabanninsu suka yi musu daga garin Maiduguri zuwa garin Marte, duk a cikin jihar Borno.

KU KARANTA: Malaman Arewa sun shirya yadda za su kawo karshen shi'a

Da misalin karfe 6 na yammane Sojojin suka fara isa filin jirgin, amma zuwa wani lokaci sai suka yi gungu gungun suna gunaguni cewa su fa ba zasu je karamar hukumar Marte ba inda aka turasu, domin kuwa a cewarsu bayan sun kwashe shekaru biyar a Maiduguri, ya kamata a mayar dasu gida.

Mayakan rundunar Sojan kasa sun yi bore, sun kulle filin sauka da tashin jirage na Maiduguri

Sojoji
Source: Depositphotos

Wani hafsan Soja da abin ya faru a gabansa ya bayyana cewa sauran manyan Sojoji ne suka shawarci babban kwamandan Sojan ta runduna ta bakwai, Bulami Biu da kada ya kuskura ya shiga filin nan saboda komai zai iya faruwa.

Majiyar ta kara da cewa da kyar aka samu aka shigar da maniyyata aikin Hajji dake filin cikin jirgi, sakamakon wannan hatsaniyar da aka samu, amma daga bisani jirgin ya tashi zuwa kasar Saudiyya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel