Zaben maye gurbi: PDP ta lashe kujerar majalisa, ta kayar da APC

Zaben maye gurbi: PDP ta lashe kujerar majalisa, ta kayar da APC

‘Yar takarar jam’iyyar PDP, uwargida Abbey Ukpukpen, ta lashe zaben maye gurbi na majalisar jihar Kuros Riba da adadin kuri’u 12,712 yayin da abokin takarar ta Ishamali Bendel na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 4,345.

Uwargida Abbey Ukpukpen, ‘yar takarar jam’iyyar PDP, ta maye gurbin mijinta, marigayi Stephen Ukpukpen, bayan ta samu nasara a zaben da aka yi jiya, Asabar a mazabar Obudu ta jihar Kuros Riba.

Ukpukpen ta samu kuri’u 12,712 ta kayar da abokin takarar ta na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 4,345.

Zaben maye gurbi: PDP ta lashe kujerar majalisa, ta kayar da APC
Zaben maye gurbi: PDP ta lashe kujerar majalisa, ta kayar da APC

Da yake gabatar da sakamakon zaben a jiya, Asabar, a karamar hukumar Obudu, baturen zabe, Dakta Frankland Briyai, ya bayyana cewar an kada jimillar kuri’u 17,303 a zaben, an samu kuri’u 607 da suka lalace.

DUBA WANNAN: Zaman Buhari shugaban kasa na har abada ne kawai zai kawo cigaba a Najeriya - Dan takarar Sanata daga arewa

Dakta Briyai ya yabawa masu kada kuri’ar bisa yadda suka fito suka yi zabe cikin lumana ba tare da hayaniya ko tashin hankali ba.

Kazalika a zaben maye gurbi da aka gudanar a jihar Katsina, kun ji cewar dan takarar Jam’iyyar APC mai mulki a zaben Sanatan Yankin Arewacin Katsina watau Honarabul Ahmad Babba-Kaita ya lashe zaben ‘Dan Majalisar da aka yi jiya Ranar Asabar. Babba Kaita ‘Dan Majalisar Jihar ne yanzu haka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng