Rikici ya barke a wurin zaben maye gurbi a jihar Bauchi, an kashe mutum guda
An samu karancin fitowar masu kada kuri’a a zaben maye gurbin sanatan Bauchi ta kudu dake gudana a yau, Asabar, 11 ga watan Agusta a kananan hukumomi 7 na jihar ta Bauchi.
A wani zagayen rangadi da wakilan jaridar Tribune suka gudanar a kananan hukumomin Dass, Tafawa Balewa da Bogoro, sun ga ‘yan tsirarin jama’ar da suka fito domin a tantance kafin kada kuri’a. Jama’ar sun shaida masu cewar yawan jami’an tsaro a wuraren zaben ne silar day a saka da dama basu fito domin kada kuri’a ba.
DUBA WANNAN: Murna da farin ciki a arewa yayin da gwamnatin tarayya ta kaddamar da babban aiki, hotuna
Wata ‘yar takara, Maryam Garba, ta jam’iyyar SDP ta koka kan cewar wasu manyan ‘yan siyasa na yawo mazabu tare da sanar da jama’a cewar ta janye takarar da take yi. Kazalika ta bayyana cewar ‘yan siyasar na sayen kuri’a ta hanyar raba kudi ga masu zabel.
Maryam ta kara da cewar ana kokarin ganin an lalata tasirin da zata iya yi a zaben ta hanyar bata mata suna tare da yada karya kanta.
Jaridar ta Tribune ta rawaito cewar an samu rigingimu a wasu mazabun tare da kisan mutun guda. Sai dai jaridar bata ambaci inda hakan ta faru ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng