Kalubalen da Gwamna Ganduje zai fuskanta a zabe mai zuwa

Kalubalen da Gwamna Ganduje zai fuskanta a zabe mai zuwa

Yayin da ake shirin zaben 2019, akwai Gwamnonin da sai sun yi da gaske domin kafar kujerar su ta na rawa. Daga cikin wadanda su ke cikin wannan sahu akwai Gwaman Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano duk da yana tare da Shugaba Buhari.

Kalubalen da Gwamna Ganduje zai fuskanta a zabe mai zuwa
Sai Ganduje yayi da gaske wajen komawa kujerar sa

Daga cikin kalubalen da Gwamnan zai fuskanta duk da irin kuri’un da ya samu da ba a taba ganin irin su a tarihin Najeriya ba akwai rigimar siyasar da ta barke a Jihar Kano kuma aka rasa wanda zai kashe wutar. Har yanzu jama'a da dama na kaunar Kwankwaso.

Manyan ‘Yan PDP irin su Ibrahim Shekarau, Rabiu Kwankwaso, Bello Hayatu Gwarzo, Aminu Wali duk za su iya kawowa Ganduje matsala.

KU KARANTA: Abin da Kwankwaso ya fada game da Ganduje wajen kamfe din PDP

1. Rikicin Kwankwasiyya

Ba sabon labari bane cewa Gwamna Abdullahi Ganduje ya samu sabani da tsohon Gwamna Mai gidan sa Rabiu Musa Kwankwaso. Hakan ba babban cikas zai iya jawo masa ba a zabe mai zuwa na 2019. Yanzu dai har Mataimakin Gwamnan Jihar Kano ya bar Ganduje.

2. Jam’iyyar PDP

Har yanzu Jam’iyyar adawa ta PDP ta na da karfi a Jihar Kano, ganin kuma kwanan nan ‘Yan Kwankwasiyya su ka shigo cikin tafiyar. Idan har PDP ta tsaida irin su Salihu Sagir Takai yana iya kawowa Ganduje matsala ganin irin Magoya bayan sa da kuma shirin da yayi a siyasance.

3. Ibrahim Shekarau

Tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau wanda shi ne Jagoran PDP a Jihar Kano yana da matukar tasiri a siyasar Kano. Yanzu haka dai Shekarau da Kwankwaso wadanda ke da tsananin ‘Yan ga-ni-kashe-ni a Kano duk ba su tare da Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng