An kashe daruruwan mutane jiya a Taraba
An kashe mutane masu dinbin yawa a wani rikici da ya barke a kauyen Kunini dake karamar hukumar Lau a jihar Taraba, yayin da wasu 'yan daba suka kaiwa wasu matasa hari a jiya
An kashe mutane masu dinbin yawa a wani rikici da ya barke a kauyen Kunini dake karamar hukumar Lau a jihar Taraba, yayin da wasu 'yan daba suka kaiwa wasu matasa hari a jiya.
Mun samu labarin cewar matasan sun fusata suma, inda suka dauki makamai suka hau 'yan daban da sara, dalilin da yasa aka samu asarar rayuka da yawa kenan, ciki kuwa harda kone gidaje da aka dinga yi sanadiyyar rikicin. Zuwan rundunar sojoji da da 'yan sanda shine ya saukaka yaduwar rikicin.
DUBA WANNAN: Anyi walkiya mun gansu: Shugaba Buhari yace yanzu lokaci ne da Allah yake ware baragurbi daga jam'iyyar APC
Wani mazaunin kauyen, Malam Dauda Bello, ya bayyana wa manema labarai cewa mata da yara da dama sun gudu sun bar kauyen yayinda sojoji ke kokarin kawo karshen rikicin a kauyen.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng