Zamu kawo karshen rashin tsaro a yankin Birnin Gwari da Zamfara - Buratai
A ranar Talatar nan ne Shugaban sojojin Najeriya, Lt. Gen Tukur Buratai yayi alkawarin kawo karshen rashin tsaron dake addabar jihar zamfara da Birnin Gwari
A ranar Talatar nan ne Shugaban sojojin Najeriya, Lt. Gen Tukur Buratai yayi alkawarin kawo karshen rashin tsaron dake addabar jihar zamfara da Birnin Gwari.
Buratai yayi wannan alkawarin ne yayin da yake zantawa da manema labarai a wata ziyarar aiki da ya kaiwa sojojin Najeriya dake Kachia da Kafanchan, dake jihar Kaduna.
Yace kudancin jihar Kaduna ta samu daidaituwa amma har yanzu akwai damuwa a Birnin Gwari da kuma jihar zamfara.
DUBA WANNAN: Kotu ta tisa keyar wasu ma'aikatan INEC zuwa gidan kurkuku
"Ba abinda ke da wahala, ku tabbatar da cewa nan ba da dadewa ba za a samu zaman lafiya a guraren.
"Mu kara tura rundunoni kuma muna kara musu kayan aiki wanda mun tabbatar cewa jami'an tsaron dake gurin zasu iya yakar ta'addanci," inji Buratai.
Yace ziyarar zai cigaba da yin ta don tabbatar da abinda rundunonin ke ciki.
Buratai yace gurin da ya kai ziyarar kwanan nan aka maida shi bataliya, mun samar da kayayyakin aiki da bataliya take bukata. Nan ba da dadewa ba zasu fara amfani.
Buratai ya ja kunnen sojojin da su zauna da shiri a kowanne lokaci domin rashin tsaron gurin yana karuwa ne.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng