Gwamnan Kaduna yayi alkawarin daukar mataki kan sha’anin tsaro bayan wani Saurayi ya ba shi shawarwari
Mun samu labari cewa a makon da ya shude ne Gwamnan Kaduna ya ji dadin wasu shawawari da wani Bawan Allah ya ba sa domin ganin an kawo karshen ta’adin da ake yi a cikin Jihar Kaduna.
Murtala Abdullahi wanda Matashi ne da yake da ilmi kan harkokin tsaro da Gidan tsaro yayi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna inda ya fadawa Gwamna Nasir El-Rufai matakan da zai bi domin maganin ‘Yan fashi da masu satar mutane a Jihar.
Murtala ya fadawa Gwamnan cewa a baza Jami’an tsaro su shiga Dajin Kaduna zuwa Abuja su yi maganin Tsagerun da ke Yankin. Bayan nan kuma ya nemi a rika sintiri tsakanin Iyakokin Jihar Kaduna da Makwabtan ta irin su Garin Abuja.
Wannan Bawan Allah ya kuma nemi a rika amfani da Dajin da ke Yankin wajen yin wasu ayyuka masu amfani domin a hana ‘Yan fashin mafaka. Murtala ya kuma nemi Gwamnatin Jihar Kaduna ta hada kai da Sojojin da ke karatu a Jaji domin inganta tsaro.
KU KARANTA: Yadda ake ta kokarin kashe ni - Sanata Dino Melaye
Ba a nan dai abin ya tsaya ba, an kuma nemi Gwamnati ta rika aiki da na’urorin daukar hoto na CCTV domin gane masu aikata wannan barna. Hakan na zuwa ne bayan Jami’an tsaron da aka baza a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna sun gaza aiki.
Tuni dai Gwamna Nasir El-Rufai yayi maraba da wadannan shawarwari da aka ba sa ta shafin Tuwita. Gwamnan yace Majalisar tsaron sa za ta duba wannan lamari kuma ta dauki matakin da ya dace domin kare rayukan al’umma a Jihar ta Kaduna.
Kun san cewa a yanzu dai fashi da makami a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna na nema ya zama ruwan dare a cikin ‘yan kwanakin nan, duk da Jami’an tsaron da aka baza a hanyar, ana tare mutane har da yamma ana fashi ko kuma ma ayi garkuwa da su.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng