Shugaba Buhari ya tura wata rundunar tsaro mai karfin gaske zuwa Zamfara

Shugaba Buhari ya tura wata rundunar tsaro mai karfin gaske zuwa Zamfara

Gwamnatin tarayya ta hada wata runduna mai dauke da jami’an tsaro 1,000 da zasu tafi jihar Zamfara domin yaki da ‘yan bindigar da suka addabi sassan jihar.

Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya sanar da hakan a yau, Lahadi, tare da bayyana cewar shugaba Buhari ne ya bayar da wannan umarni.

Rundunar jami’an tsaron ta hada da dakarun sojin kasa da na sama, ‘yan sanda da kuma Civil Defence.

Shugaba Buhari ya tura wata rundunar tsaro mai karfin gaske zuwa Zamfara
Shugaba Buhari

Garba Shehu ya kara da cewar tuni dakarun sojin sama suka fara jigilar jiragennsu ya zuwa filin tashi da saukar jirage dake jihar Katsina mai makwabtaka da jihar ta Zamfara.

DUBA WANNAN: An cafke malamin addini da ya sace manjo a hukumar sojin Najeriya

Shugaba Buhari ya bayar da umarnin yin amfani da wasu jiragen yaki masu dauke da wasu na’urorin zamani domin samun dammar gano wuraren da ‘yan ta’addar ke buya. A cewar Garba Shehu, yin hakan ya zama tilas ne saboda gaggauta takaita yawan barnar da ‘yan bindigar ke tafkawa a jihar.

Fadar shugaban kasa ta gargadi kafafen yada labarai da su gujewa yada labaran da basu inganta ba ko marasa tushe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng