An kone daya daga cikin 'yan fashin da suka kashe wata kyakykyawar budurwa, duba hoto
A jiya Juma'a ne wasu 'yan fashi da makami suka kashe wata budurwa mai suna Njoku Uchechi a wata fashi da su kayi kusa da Diamond Bank dake Suru-Alaba dake Legas.
'Yan fashin sun tare ta bayan ta fito daga bankin sannan suka harbe ta a kai. Sun kuma yi awom gaba da zunzurutun kudi N150,000 data ciro daga bankin.
Sai dai wasu mutane dake wucewa ta hanyar sunyi nasarar kama daya daga cikin 'yan fashin yayin da daya dan fashi ya tsere da kudaden.
DUBA WANNAN: Da dumi-dumi: Shuagaba Buhari zai tashi zuwa birnin Lome a yau, duba jerin ‘yan rakiyar sa
Bayan kama shi, mutane sunyi masa duka har ya kasa motsawa sannan suka dauko tayoyin mota suka makalla masa suka banka masa wuta.
Tuni dai an kai gawar marigayiyar dakin ajiye gawawaki na asbiti.
Mutane da dama sunyi jaje game da rasuwar budurwar wanda haka siddan 'yan fashin suka tare ta kuma suka halaka ta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng