Tayi wurgi da gawar mijinta waje, tace ba za'a ajiye mata gawa a daki ba
Masu zaman makoki sun watse da mamaki inda mata ta wurga akwatin gawar mijin ta waje da cewa ba zai kara kwana a gidan da suka rayu ciki tare ba
Masu zaman makoki sun watse da mamaki inda mata ta wurga akwatin gawar mijin ta waje da cewa ba zai kara kwana a gidan da suka rayu ciki tare ba.
Kamar yanda majiyar mu ta sanar mana, gawar mamacin mai suna Dominic Makoreke ta kwana a waje ne inda ake zuga ruwan sama saboda matar shi mai suna Betty ta hana gawar tashi kwana a Aidan.
DUBA WANNAN: An nada sabon jakadan Najeriya a birnin New York
Mun samu labarin cewa Makoreke ya saki Betty domin zai auri wata.
Daya daga cikin masu zaman makokin yace sun samu gurin fakewa ne su da akwatin da gawar mamacin take ciki kafin ruwan ya tsaya. Dukkanin mu masu zaman makokin mun tozarta, mun ma rasa yanda zamuyi, inji masu zaman makokin.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng