2019: INEC ta nada sabbin kwamishinonin zabe a jihohin arewa 2, duba hotuna
A yau, Laraba, ne shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmoud Yakubu, ya nada tare da rantsar da sabbin kwamishinonin zabe 2 da ya nada.
Sabbin kwamishinonin 2 da aka nada zasu yi aiki ne a jihohin arewa 2 da suka hada da Naija da Zamfara.
Sabbin kwamishinonin zaben sune; Ahmad Bello Mahmud (Jihar Zamfara) da Garba Attahiru Madami (jihar Neja).
An rantsar da sabbin kwamishinonin ne a ofishin hukummar zabe na kasa dake birnin tarayya, Abuja.
DUBA WANNAN: Jerin sunayen 'yan majalisar dokoki 6 na jihar Kano da zasu bi Kwankwaso PDP
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud, ya taya su murna zabensu da kuma tabbatar da su a matsayin sabbin kwamishinoni tare da yin kira garesu su kasance masu riko da rantsuwar suka yin a yin aiki da gaskiya da rikon amana.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng