Wani ya yiwa mahaifiyarsa yankan rago saboda ya gaji filayenta

Wani ya yiwa mahaifiyarsa yankan rago saboda ya gaji filayenta

A yau Laraba mutanen kauyen Okpunoeze dake Uraugu, Nwewi sun tashi da bakin cikin saboda wani matashi Chinedu Ikegwuonwu mai shekaru 40 ya kashe mahaifiyarsa Mrs Bene Ikegwuonwu mai shekaru 70 a duniya.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta gano cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 8 na safe bayan sun samu sabani a kan fili mallakin kanin wanda ake zargi da aikata kisan.

Wani mazaunin kauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa majiyar Legit.ng cewa Chinedu ya lalabo ta baya ne yayin da mahaifiyarsa ke girki ya yi mata yankan rago da adda.

Da ya kashe uwa tai saboda ya gaji filayenta
Da ya kashe uwa tai saboda ya gaji filayenta

"Bayan ya halaka mahaifiyarsa, wanda ake zargin ya tsere ya bar matarsa da dan sa guda," kamar yadda majiyar ya zayyana.

KU KARANTA: Shugaba Buhari bashi da ikon dakatar da binciken da ake yiwa Saraki

Rahottani sunce marigayiyar tana da yara maza hudu da mata uku, daya daga cikin 'ya'yan ya rasu kwanakin baya sakamakon hatsarin mota.

Wani dan uwan marigayiyar wanda ya nemi a boye sunansa yace wanda ake zargin ya dawo daga fatauci ne daga garin Aba kuma bai samu sa'a ba.

Majiyar ya kara da cewa wanda ake zargin ya dade yana artabu da mahaifiyarsa saboda yana son ya kwace filin kaninsa.

"Mahaifiyar Chinedu ta kara masa kudi saboda ya tayar da gininsa amma duk da haka bai fara komai ba a filin. Har ta dauki kudi daga asusun ajiyar diyar ta ta bashi amma duk da haka ya tubure sai ya karbe filin kaninsa," inji majiyar.

Jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan, Mr Haruna Mohammed ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya kara da cewa hukumar ta baza jami'anta domin kamo wanda ake zargin don gudanar da cikaken bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164