Sauya shekar Kwankwaso zuwa PDP alheri ne ga Ganduje - Iliyasu Kwankwaso

Sauya shekar Kwankwaso zuwa PDP alheri ne ga Ganduje - Iliyasu Kwankwaso

Kwamishinan raya karkara na jihar Kano, Alhaji Iliyasu Musa Kwankwaso, a ranar Talatar ta yau ya bayyana cewa, ficewar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso daga jam'iyyar APC zuwa PDP alheri ga gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A yayin tofa albarkacin bakin sa dangane da ficewar dan uwan sa daga jam'iyyar su ta APC Iliyasu Kwankwaso ya bayyana cewa, tuni suka sanyawa Kwankwaso rigar adawa sakamakon zawarcin jam'iyyar PDP da yake faman aiwatar wa watanni shida da suka gabata.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Iliyasu Kwankwaso ya bayyana cewa wannan lamari ba zai yi wani tasiri ga gwamna Ganduja ba hasali ma alheri ne a gare sa dangane da samun nasara a zaben 2019.

Sauya shekar Kwankwaso zuwa PDP alheri ne ga Ganduje - Iliyasu Kwankwaso

Sauya shekar Kwankwaso zuwa PDP alheri ne ga Ganduje - Iliyasu Kwankwaso

A cewar sa, cin moriyar ganga da Kwankwaso ya yiwa jam'iyyar APC babban alheri ne a gare ta sakamakon yanayi da salon sa na siyasa tamkar kudan zuma da sai da wuta akan sha kashin sa.

Ya ci gaba da cewa, ko shakka babu Kwankwaso zai kasance wani jigo na jam'iyyar PDP a jihar Kano, inda zai taka rawar gani tare da hadin gwiwar tsohon Ministan ilimi kuma tsohon gwamnan jihar, Mallam Ibrahim Shekarau, tsohon ministan harkokin kasashen ketare, Ambasada Aminu Wali da kuma Sanata Bello Hayatu.

Legit.ng ta ruwaito cewa, a yau ne jam'iyyar APC ta rasa kimanin 'yan majalisar tarayya 50 da suka sauya sheka zuwa wasu jam'iyyun adawa musamman jam'iyyar PDP, wanda Kwankwaso na daya daga cikin wadanda suka raba gari da ita.

KARANTA KUMA: Sai an ɗauki tsawon shekaru 22 na gyaran ɓarnar Aregbesola - Omisore

Kwamshinan ya kara da cewa, sai dai Kwankwaso ba abin dogaro bane cikin kowace jam'iyya sakamakon yadda yake kasancewa tamkar kwai bara gurbi mai janyo lalata ga makusanta cikin jam'iyyar da duk ya tsinci kansa cikin ta.

Bugu da kari ya kara da cewa, cikin watanni kalilan masu gabatowa za a sha mamakin yadda da yawa daga cikin mambobin jam'iyyar ta PDP za su fara tserewa da diga-digan su sakamakon kasancewar Kwankwaso da ya sanya riga irin ta su a halin yanzu.

Ya kuma jaddada cewa, Sanata Kwankwaso yaudara kurum yake ga al'umma ta neman kujerar shugaban kasa amma ba ya da wata manufa face sake maye gurbin kujearar sa ta Sanata a majalisar dattawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel