Yanzu Yanzu: Rundunar sojin ruwan Najeriya sun fara daukar ma’aikata
Rundunar sojojin ruwa na Najeriya ta fara shirye-shiryen daukan yan Najeriya da suka kammala karatu aiki.
Za’a iya ganin tsarin daukar ta shafin rundunar sojin ruwa na yanar gizo wato www.joinnigeriannavy.com wanda za’a bude a gobe, Laraba 11 ga watan Oktoba ga masu sha’awar yin aikin.
Ya zama lallai masu sha’awar aikin su kasance yan Najeriya, sannan kuma su samu sakamakon jarabawar digiri mai kyau akalla (Second Class Upper Division) sannan kuma ga masu shaidar HND su samu (Upper Credit).
KU KARANTA KUMA: Cutar ‘Monkey Pox’ ya yadu zuwa jihohi 7 na kasar nan
Maza su kasance tsawon su ya kai akalla mita 1.68 yayinda kuma mata zasu kasance akalla mita 1.65. Sannan kuma shekarun su ya kasance tsakanin 22 zuwa 28 a ranar 31 ga watan Janairun 2018, sai dai ga limami da karda su wuce shekaru 30 a ranar 31 ga watan Janairun 2017.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng