Gutsuri tsoma: Sakon whatsapp da ake yadawa ya jawo kashe-kashe
- Mutane da ywa na son yada gulma komai dacinta ga al'umma
- Wasu lokuta abin kan yadu kamar wutar daji
- Lamarin kan kai ga kashe-kashe musamman a kasashe masu tasowa
Bayan Najeriya, inda ake yawan son yada zantuka ko na gaskiya ko na karya a shafukan sada zumunta, sabodayawan masu zaman sa ido da masu zaman kashe wando, haka ma a Indiya, inda ake samun labarai na karya a shafukan sada zumunta kamar fesbuk da tuwita da ma whatsapp.
Yanzu haka ma, ana can ana yada zantukan yan mata na masu son junansu inda ake bata musu suna ana kuma kira da ayi musu hukunci mai tsanani.
Labarin da ke fitowa daga Indiya ma kuma, na nuna irin wannan yada labaran karya, da jita-jita, ya kai ga kisan wasu da basu ji ba basu gani ba wai don an yada hotonsu da cewa wai suna satar yara.
DUBA WANNAN: Zata mayar da sadaki don a raba auren shekaru 8
Wani Ba'Indiye mai shekara 32 wanda injiniyar kwamfuta ne ya kasance mutum na baya-baya nan daya fada hannun gungun mutane masu daukar doka a hannunsu, sakamakon zargin satar yara da aka yi masa wanda aka yada a shafin sada zumuntar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng