Da dumin sa: 'Yan ta'addan Boko Haram sun tafka babbar ta'asa a wasu kauyukan Borno
Akalla mutane 30 ne suka rasa rayukan su yayin da kuma da yawa suka bace bat har yanzu ba'a gansu biyo bayan wani mummunan harin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai wa wasu matafiya akan hanyar Dikwa zuwa Ngala a jihar Borno.
Wani ganau ya shaidawa majiyar ta Daily trust a wayar tarho cewa akalla motoci 27 ne dauke da mutane da kayayyakin masarufi 'yan ta'addan suka tare suna harbi kafin daga bisani mutanen ciki su tsere.
KU KARANTA: Sunayen attajiran Afrika a 2018
Legit.ng ta samu cewa sai dai har yanzu mahukunta a jami'an tsaron ba su ce uffan ba game da lamarin kuma duk kokarin da akayi don jin ta bakin su ya citura.
A wani labarin kuma, Ana cigaba da takaddama a tsakanin majalisar tarayyar Najeriya da kuma shugaban kasa game da wani sabon kasafin kudin da yakai don su amince masa na kudaden da hukumar zabe ke bukata don gudanar da zabukan 2019.
Kamar yadda muka samu daga majiyar mu, a cikin sabon kasafin kudin, jami'an tsaron kasar da suka hada da 'yan sanda da kuma masu tsaron farar hula na Nigeria Security and Civil Defence Corps sunce suna bukatar zunzurutun kudi har Naira miliyan 317 don ciyar da dabbobin su abinci.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng