Najeriya na asarar N900m a kullum idan ana saida lita naira 145
Rahotanni dake zuwa sun nuna mana cewa karamin ministan man fetur, Ibe Kachikwu ya sanar da cewa kasar Najeriya ta yi asarar naira biliyan 55.5 sanadiyan shigo da tataccen man fetur da ake saida wa kan naira 145 kowace lita.
Duk da cewar Kachikwu ya bayyana cewa ba za a kara farashinlitar man fetur ba wanda ke kan naira 145 ba, sai dai kuma ya ce a baya a cikin 2016, an yanka wa lita daya farashin 145 ne, lokacin ana sayar da kowace gangar danyen fetur kan dala 49. Yanzu kuwa ya ce ana sayar da ganga dala 67, don haka wancan farashi na 145 ba mai dawwama ba ne.
Da ya ke jawabi a gaban kwamitin harkokin fetur, Kachikwu ya ce a da kowace lita na kamawa naira 133.28, tun daga sayo ta daga waje har sauke ta a daffo-daffon NNPC. Amma a yanzu lita daya na kamawa naira 171 har saukewa.
Ya ce dalili kenan a yanzu babu mai iya shigo da fetur daga waje idan ba NNPC ba. Kachikwu ya ce a haka ake shigo da fetur ana faduwa naira 26 a kowace lita, kuma a kullum ana shigo da lita miliyan 25.
Kachikwu ya ce tun daga cikin watan Oktoba zuwa yau, a kullum Najeriya na yin asarar naira milyan 800 zuwa 900 idan ta saida lita daya kan naira 145.
KU KARANTA KUMA: Ortom ya dauki babban mataki yayinda ake ci gaba da kashe-kashe a jihar Benue
Ya ce wasu hanyoyin da aka yi taro domin samowa don a magance wannan matsala kafin nan da watanni 18 da za a fara aiki da kanana matatan man mu, su ne gwamnati ta yi wa ‘yan kasuwa masu shigo da mai rangwamen dala, a rika sayar musu a kan naira 204, maimakon yadda a yanzu Babban Bankin Najeriya, CBN ke saida musu a kan naira 305.
Ya ce ta haka ne kawai za a iya sayar da fetur a kan naira 145 nan gaba.
“Ko kuma kawai gidajen mai na NNPC su rika sayarwa a kan naira 145, su kuma na ‘yan kasuwa su sayar duk yadda su ka ga dama."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng